1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kafa gwamnati tsakanin 'yan adawa da sojojin Sudan

Mahmud Yaya Azare SB
July 5, 2019

Yarjejeniyar kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadin gwiwa tsakanin sojoji masu mulkin Sudan da gamayya na 'yan adawa da kwadagon kasar saboda kare manufofin juyin-juya hali.

https://p.dw.com/p/3LeWN
Sudan Karthoum | Demonstranten feiern nach einigung von Generälen und Protestführern
Hoto: Getty Images/AFP/A. Shazly

Yarjejeniyar da aka cimma albarkacin shiga tsakanin Tarayyar Afirka da kasar Habasha da ke zuwa bayan an share watanni ana kai ruwa rana tsakanin Majalisar Sojin ta Sudan da masu fafutuka za ta kai ga kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadaka tsakanin bangarorin, kamar yadda wakilin Tarayyar ta Afirka, Mohammed el-Hassan Labat ya tabbatar.

Sudan Khartum Abraq | Mitglieder der RSF - Rapid Support Forces
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Ita dai wannan sabuwar gwamnati da za'a kafa  da zata kwashe shekaru 3 da yan kai a karagar mulki kafin gudanar da zabe, sojoji zasu jagorance ta na tsawan watanni 18, kafin mikawa fararen hula suma su riketa na tsawan wasu watanni 18.

A daya bangaren ,Mataimakin shugaban majalisar sojin kasar, Janar Mohammed Hamdan Dagalo, wanda kafin cimma yarjejeniyar ya shirya gangamin masu goyan bayan sojoji, ya bayyana cewa, wannan yarjejeniyar ta gama gari ce.

Shi kuwa kakakin masu Fafutuka, Umar El-Dugair, nuna mahimmanci wannan yarjejeniyar ya yi wajen yin aiki don cire kitse daga wuta ga 'yan kasar.

Kazalika yarjejeniyar ta amince da kafa kwamiti mai zaman kansa da zai gudanar da binciken ba sani ba sabo saboda ganin kwakwaf  kan kashe-kashen masu zaman dirshan da zanga-zangar da suka biyo bayan tsige Shugaba Omar Al-Bashir daga mulki, wanda ya kai ga kasha kimanin mutune 250.

Zehntausende Menschen marschieren in Khartoum auf den Straßen
Hoto: Reuters/U. Bektas

Tuni dai yan kasar suka banzama kan tituna suna ta shagulgulan murna da cimma wannan yarjejeniyar da wasu ke dauka a matsayin kama hanya ce ta cimma muradun juyin-juya hali:

To sai dai duk da hakan, gamayyan kungiyoyin 'yan kwadagon kasar da ta jagoranci zanga-zangar ta nemi 'yan kasar da su guji kwanciya da sirdi, su tsaya cikin shiri, don kar a yi musu sakiyar da ba ruwa.