Gwamnati ta yi sulhu da 'yan tawaye
February 5, 2019Talla
Tun bayan hambare gwamnatin tsohon shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Francois Bozize daga mulki a shekarar 2013, kasar ke fama bulluwar kungiyoyin sa kai masu dauke da makamai, wadanda ke rike da kashi 80 cikin dari na fadin kasar.
Yarjejeniyar wacce ke karkashin jagorancin kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, ta kai ga shawo kan kungiyoyin ‘yan tawaye 14 da ke gwaggwarmaya ya zuwa ga samun masalahar ne, kwanaki bayan an yi hannun riga kan batun raba mukamai da batun yafiya ga shugabannin kungiyoyin masu yakin sunkuru.