1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu

January 24, 2014

Ka'idojin yarjejeniyar sun hada da sakin wasu 'yan siyasa da ake tsare da su da kuma janye dakarun Yuganda daga kasar.

https://p.dw.com/p/1Awj7
Unterzeichnung Waffenstillstandabkommen für Südsudan in Addis Abeba Äthiopien 23.01.2014
Hoto: picture-alliance/dpa

A wannan makon ma jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne a kan kasashen Sudan ta Kudu da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A labarinta mai taken an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, jaridar Frankfurter Allgemeine Zeritung cewa ta yi:

" Gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha wato Ethiopia, inda tun a fakon watan Janeru masu rikici da junan ke tattaunawa. Kawo yanzu an kasa cimma matsaya ne saboda bukatun 'yan tawaye na a sako wasu mutane 11 na kurkusa da tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar, da ake tsare da su a Juba, babban birnin kasar. Amma yanzu gwamnati ta amince ta saki mutane. Yarjejeniyar tsagaita wutar ta kuma bukaci janyewar sojojin Yuganda da aka girke a Sudan ta Kudu tun bayan barkewar rikicin a tsakiyar watan Disamba, kuma suke mara wa dakarun gwamnati baya."

Rikici na ci gaba a Afirka ta Tsakiya

Ta'addancin sojojin sa kai a kan Musulmi inji jaridar die Tageszeitung tana mai mayar da hankali kan rikicin da ya ki ya ki cinyewa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya duk da rantsar da sabuwar shugabar kasa a tsakiyar wannan mako.

Zentralafrika Milizkämpfer Soldat 23.01.2014
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

"Kwanaki biyu kacal bayan zaban Catherine Samba-Panza a matsayin sabuwar shugabar wucin gadi, hare-haren da ake kai wa Musulmi tsiraru a birnin Bangui sun kai kololuwa. Tun da sanyin safiyar ranar Laraba 'yan bangar kungiyar Anti-Balaka suka yi kaca-kaca da unguwar PK 13 inda Musulmi 'yan ci-rani ke da zama da ke a wajen gari. Wannan mummunan harin tare da kwasar ganima da 'yan Anti-Balaka ke yi a kan Musulmi, ya nuna a fili cewa ba sa kaunar ganin Musulmi a cikin kasar. Kuma da wannan sabon farmakin sojojin sa kan na Kirista na nuna cewa yanzu suke kan kujerar mulkin kasar. Tun bayan murabus din Michel Djotodia daga mukamin shugaban riko a ranar 10 ga watannan na Janeru, sojojin sa kai na Anti-Balaka ke ganin sun samu wani kwarin gwiwa, su kuma Musulmi sun yi rauni a fagen siyasa, musamman tun lokacin da sojojin Faransa suka mayar da hankali wajen kwancen damarar mayakan kungiyar Seleka a farkon watan Disamba. A saboda wannan halin da kasar ke ciki, sabuwar shugabar wucin gadin na da jan aiki wajen dinke barakar da ke tsakanin al'ummomin kasarta."

Koma bayan ga demokradiyya a wasu kasashe

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung labari ta buga game da sakamakon wani nazari da gidauniyar Bertelsmann ta nan Jamus ta yi, a kan ci-gaba ko akasin haka a duniya.

Forum InnovAfrica Elfenbeinküste Abidjan
Matasa a wani taron kara wa juna sani a AbidjanHoto: DW/S. Martineau

"Manazarta sun yi nuni da cewa kasashe da yawa a duniya na kara komawa baya a fannin demokradiyya, musamman kasashen Larabawa da na gabacin nahiyar Turai. To sai dai abin mamaki, ana samun gagarumin ci-gaba a kasashe matalauta na yankin yammacin Afirka. Binciken da gidauniyar ta yi, ta kuma gano cewa tun a shekarar 2012 abubuwa sai kara lalacewa suke a da yawa daga cikin kasashen duniya. A Afirka sun ba da misali da kasashe irinsu Angola, Guinea da kuma Mali. Sai dai kasar Cote d'Ivoire a cewar masanan, ta samu gagarumin ci-gaba a fannin girke demokradiyya da tsarin mulki na doka a tsukin shekaru takwas da suka wuce, duk da yakin basasa da ta yi fama da shi."

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman