Yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
February 2, 2015Masu shiga tsakani na kungiyar kasashen Afrika ta AU suka ce yarjejeniya ta fayyace irin hanyar da za a bi wajen samun zaman lafiya da kuma yadda bangarorin biyu za su yi rabon mukamai da zarar sun girka gwamnatin rikon kwarya inda Mr. Kiir zai cigaba da kasancewa shugaban kasa yayin da Machar zai zame masa mataimaki.
To sai dai duk da wannan 'yan tawayen sun ce dole ne a kara tsefe abubuwan da wannan yarjejeniya ta kunsa, inda Machar ya ce bangarorin biyu za su yi wani zama don tantance irin mukaman da kowa zai samu a ita wannan gwamnati da suke son ganin an samar.
A watan Janairun shekarar da ta gabata ma dai an kai ga cimma irin wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan tawayen na Sudan ta Kudu sai dai kafin tafiyar ta yi nisa bangarori biyun suka zargi juna da yin karen tsaye ga tanade-tanade yarjejeniyar.