1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar tsagaita wuta na aiki a Sudan

Mouhamadou Awal Balarabe
April 25, 2023

Bangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun fara mutunta sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma, sabanin makamanciyar wannan yarjejeniya ta kwanakin da suka gabata da suka yi fatali da ita .

https://p.dw.com/p/4QViL
Mayakan rundunar RSF sun tsagaita wuta a SudanHoto: Hussein Malla/AP/dpa

Wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta fara aiki da sanyin safiyar wannanTalata a Sudan, bayan da aka shafe kwanaki goma ana gwabzawa fada tsakanin bangarorin da ke gaba da juna. Sojojin Sudan da dakarun rundunar ko ta kwana ta RSF sun amince da hakan ne bayan "tattaunawa mai zurfi", kamar yadda sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ya sanar.

Ana sa ran tsagaita wutar za ta dauki tsawon sa'o'i 72. Amma dai an taba cimma irin wannan yarjejeniya a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, ba tare da bangarorin biyu sun mutunta ta ba. A cewar kungiyar Tarayyar Turai dai, yanzu haka ana ci gaba da kwashe 'yan kasashen EU kusan 1,500 daga Sudan, yawancinsu daga sojojin Jamus na Bundeswehr.