1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau ake zaben tsakiyar wa'adi a Amirka

November 8, 2022

A kasar ta Amirka, a wannan zaben ne ake zaben dukkan 'yan majalisar wakilai, da kashi daya bisa uku na majalisar dattawa da kuma wasu mukaman shugabancin jihohi da dama.

https://p.dw.com/p/4JBWu
USA Georgia Wahlen Midterms 2022
Hoto: CHENEY ORR/REUTERS

A yau Talata ne ake muhimmin zaben nan na tsakiyar wa'adi a Amirka, zaben da ke matsayin mai gwada kimar gwamnatin Shugaba Biden mai ci da kuma wanda ya gada Donald Trump.

Jam'iyyar Democrats ta Shugaba Biden dai na fadi tashin ganin ta samu rinjaye a majalisar dokoki, daidai lokacin da jam'iyyar Republicans ta tsohon Shugaba Trump ta yi yakinneman zabe da batun tsadar rayuwa da kuma karuwar aikata manyan laifuka a Amirkar.

Saboda wasu 'yan matsalolin da gwamnati mai ci ke ciki, masana siyasa na ganin zaben na tsakiyar wa'adi, zai kasance babban manuniya ga karbuwar da shugaban mai shekaru 79 ke da shi a Amirka.

Da Shugaba Biden da ma tsohon shugaba Donald Trump dai, dukkanin su suna son sake tsayawa takara a 2024.