Yawan 'yan gudun hijirar Siriya na karuwa
September 30, 2014Talla
Ms Amos ta shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya cewar irin kutsa kai da mayakan IS din suka yi a arewacin Aleppo yanzu haka ya tilastawa kimanin mutane dubu 160 kauracewa matsugunansu, inda galibinsu suka gudu kasar Turkiyya don tsira da rayuwarsu.
Daga cikin wanda suka tserewa rikicin inji Amos mafi yawansu mata ne da kananan yara kuma halin da suke ciki na da tada hankali kana yanayin da aka shiga ya sanya kai kayan agaji gare na da matukar wahala.