1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Gaza

November 17, 2012

Mutane fiye da 40 sun rasa rayuka a cikin hare-haren da Isra'ila da Hamas ke kai wa juna.

https://p.dw.com/p/16l3X
An explosion and smoke are seen after Israeli strikes in Gaza City November 17, 2012. Israeli aircraft pounded Hamas government buildings in Gaza on Saturday, including the building housing the prime minister's office, after Israel's Cabinet authorised the mobilisation of up to 75,000 reservists, preparing the ground for a possible invasion into Gaza. REUTERS/Suhaib Salem (GAZA - Tags: CIVIL UNREST MILITARY POLITICS TPX IMAGES OF THE DAY)
Hoto: Reuters

Rundunar tsaron Isra'ila na cigaba da kai hare-hare ta sararin samaniya a zirin Gaza.

Daya daga wannan hari yayi kaca-kaca da cibiyar ƙungiyar Hamas da kuma ofsihin ministan cikin gida.

Ya zuwa wannan lokaci aƙalla mutane 40 sun rasa rayuka a Gaza, sannan uku sun kwanta dama a ɓangaren bamni Yahudu sanadiyar rokokin da Hamas ta cilla.

Bayan Firayim ministan Masar, shima ministan harkokin wajen Tunisiya, Rafik Abdel Salam ya kai ziyara zirin Gaza a wannan Asabar, inda ya taya gazawa alhini.

Gwamnatin Isra'ila ta umurci sojoji dubu 75 shiga cikin shirin takwana, a wani mataki na yunƙurin kai farmaki ta ƙasa a Gaza.

A wani jawabi da ya yi a birnin Alƙahira, Faramiyan Turkiyya Recep Tayib Erdogan, yayi tur da Allah wadai da matakin da Isra'ila ta ɗauka kan zirin Gaza.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu