Jamus: An kawar da wani harin ta'addanci
December 7, 2022Talla
Tuni da 'yan sanda sun kama mutane 25 a fadin kasar sannan ana gudanar da bincike a kan wasu karin mutane 130. Ministan shari'a na Jamus Marco Buschmann ya bayyana a shafinsa na Twitter cewa, ana zargin mutane da shirya kai hari da makamai da nufin kifar da gwamnati. A cewar ofishin mai gabatar da kara, daya daga cikin wadanda suka kitsa mkarkahiyar ya tuntubi wakilan Rasha a Jamus. To amma jum kadan bayan wananan sanarwa ofishin jakadancin Rasha a Jamus ya musunta zargin yana mai cewar ba su da alaka da 'yan ta'adda. A halin da ake ciki an baza jami'an tsaro kusan dubu uku a fadin jamus,sannan an kama wasu mutanen a Italiya da Autiriya.