Yiwuwar ɗorewar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu
January 24, 2014Duk da cewa gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, masu sharhi kan al'amura na gargaɗin cewa zai yi wuya a shawo kan 'yan tawayen dake ɗauke da makamai a kuma tabbatar da ɗorewar wannan yarjejeniya. Ko a wannan juma'ar 'yan tawayen sun zargi dakarun sojin ƙasar da kai musu hari, zargin da sojojin suka ƙaryata.
Da yamacin jiya alhamis ne ɓangarorin dake yaƙar juna suka rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar a babban birnin ƙasar Ethiopia wato Adis Ababa. Wakilan shugaban ƙasa Salva Kiir da 'yan tawayen dake goyon bayan hamɓararren mataimakin shugaban ƙasa Riek Machar, a ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ci gaban tattalin arziƙin ƙasashen Afrika wato IGAD.
Aƙalla mutane dubu 10 ake kyautata zaton sun hallaka a rikicin da ya haɗa daarun da ke goyon bayan shugaba Kiir da ƙawancen sojojin da suka bijirewa gwamnati da ma ƙungiyoyin tawayen da ke ƙarƙashin jagorancin Machar wanda aka san shi a matsayin wani fitaccen mai yaƙin sunkuru
Martanin masu shiga tsakani
Seyoum Mesfin shi ne jakadar ƙungiyar IGAD wajen sassanta wannan rikici kuma ya kwantanta sanya hannun da aka yi kan wannan yarjejeniya a matsayin wani babban mataki na kawo ƙarshen wannan bala'i kuma ya nuna cewa mun yi la'akari da irin uƙubar da aka jefa talakawa ciki, kuma ya yi kira da a tabbatar da cewa wannan yarjejeniya ta ɗore
"Ina jaddada cewa yarjeniyoyin sulhu da dama ne akan ƙulla amma kuma ƙalilan ne sukan ɗore, haka nan kuma wannan lamari na iya samar da sulhu da kwanciyar hankali na wani gajeren lokaci ne kafin a asake komawa gidan jiya ba mu so haka ya kasance a Sudan ta Kudu. Zan kuma ƙara da cewa ƙalubalen da zai biyo baya wata ƙila ma yafi lokacin yaƙin domin sassantawa zai iya kasncewa da sarƙaƙiya, domin mutane da yawa suka sadaukar da rayukansu saboda ƙasar ta sami 'yancin kanta"
Buƙatar gudanar da taron ƙasa
Ko ga waɗanda suka sanya ido kan rikicin ikon na Kudancin Sudan wanda ke tattare sarƙaƙiya musamman yadda ya lalace har ya kai ga maƙoci yana far ma maƙoci, rigingimun sun ƙazance cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. To amma ana fata wannan yarjejeniya za ta buɗe sabon babi ya kuma share hanyar gudanar da taron ƙasa saboda irin yanayin da aka shiga yanzu. Seyoum Mesfin jakadan ƙungiyar IGAD wajen sassanta wannan rikici shi ma ya bayyana wannan buƙatar
"Akwai buƙatar a gudanar da tattaunawar ƙasa ba tare da an bar kowa a baya ba ƙungiyar IGAD da ƙungiyar Tarayyar Afirka muna aiki tare da al'ummar ƙasa da ƙasa domin taimaka muku da kuma mutanen Sudan ta Kudu ba zamu gaza ba sai dai idan ku ne za ku sa mu mu gaza"
Fargaban 'yan ƙasa
Akwai 'yan ƙasar da dama dake da ra'ayin cewa ɗaukar mataki na siyasa ko kuma ma yin alƙawarin raba iko nan gaba zai taimakawa waɗanda dama suka saba amfani da makamai wajen samun muƙaman siyasa. Kuma da yawa na ganin cewa mai yiwuwa yarjejeniyar ba za ta yi tasiri basaboda a ra'ayinsu ƙiyayyar da ke tsakanin ƙabilar Dimka na shugaba Kiir waɗanda kuma suka fi yawa a ƙasar, da ƙabilar Nuer na Machar ya kai wani yanayi da sai dai ikon Allah. A dalilin haka ne ma jagoran wakilan gwamnati wajen sassantawan Nhial Deng Nhial ya ce yana shakkun ko za su iya shawo kan mayaƙan 'yan tawayen
"Ganin cewa yawancin mayaƙan fararen hula ne, wadanda ba su da tarbiyar soji saboda haka ba lallai ne su bi umurnin kwance ɗammara ba, wannan kuma zai iya mayar da hannun agogo baya, saboda haka muna roƙon IGAD da al'ummar ƙasa da ƙasa su sa ido sosai a wannan matsala, idan ba haka ba yunƙurin samar da sulhu ba zai samar da ɗa mai ido ba"
Tun 15 ga watan Disemban bara sabuwar ƙasar Afirkan ta shiga wannan hali, kuma duk da irin shawarwari da maƙudan kuɗin da al'ummomin ƙasa da ƙasa suka zuɓa a ƙasar bayan da ta fito daga yaƙin basasa a shekarar 2005 ba a iya an kauce daga wannan bala'in da ya sake durƙusar da ƙasar ba.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu