1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin agazawa 'yan gudun hijira

Larwana Malam Hami/USUMay 7, 2015

Kungiyoyi bada tallafi masu zaman kansu sun fara isa ga 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa don ba su agajin gaggawa.

https://p.dw.com/p/1FMVH
Flüchtlingslager in Bama, Nigeria
Hoto: Reuters/S.Ini

A yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar, kungiyoyin agaji na cikin gida
da suka hada da Red Cross ko kuma Croix Rouge, tare da ban hanun kungiyoyin kasa da kasa, sun kaddamar da taimakon gaggawa ga 'yan gudun hijirar tapkin Chadi. Inda rohotanni ke nunin cewar yawan su ya doshi kimanin 20.000. Kawo yanzu dai kafofi na ci-gaba da kasance wa a bude, ga duk wani mai hanu da shuni game da batun kawo ma 'yan gudun hijiran dauki.

Rabon taimakon gaggawar da kungiyoyin agajin na ciki da wajen
kasar ta Jamhuriyar Nijar suka kaddamar a yankin na Diffa, gundumar
Gegime, wace ke daya daga cikin yankunan da matsalar hijirar
ta yi gamari: Biyo bayan cikar wa'adin takaitacciyar dokar ta-baci, ta karauce ma tsibiran tapkin Chadi bangaren Nijar. Alhaji Abdullaye Ada, shi ne shugaban kungiyar Croix Rouge ta kasa shiyyar jihar Diffa. Yabayyana cewa suna iya kokarinsu don bada tallafi ga yan gudun hijiran.

Wasu 'yan gudun hijira da suka fito daga tsibirai daban-daban
na kewayen tapkin na Chadi, wanda kuma suke zaman hijira a garin
Gegimi a zantawarsu da wakilin DW Larwana Malam Hami sun bayyana cewa hakika suna matukar bukatar samun tallafi.

Daga farkon rikicin zuwa wanan lokaci gwamnatin kasar Nijar da kungiyoyin agaji, na taka iya ta su rawa a kokarin su na ceto rayuwar
mazauna tsibiran.Kamar yadda Alhaji Abubakar Gamandi shugaban kungiyar masunta da dilalan kifi a a yankin tapkin Chadi baki daya ya bayyana gamsuwarsa bisa aikin agajin baki daya.

Daga mai karamin karfi izuwa masu karfin fada aji a tsibiran
dai, rohotanni a cewar a yanzu lamarin ya zama in ba ka yi ba bani wuri, inda kowa ke ta kansa don neman tsira da rayuwarsa.

Nigerien Maiduguri Autobombe Doppelanschlag März 2014
Hoto: Getty Images/AFP