1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin daidaita rikicin Sudan Ta Kudu

Ahmed SalisuFebruary 2, 2015

Duk da shakkun da jama'a ke yi dangane da yiwuwar dorewar yarjejeniyar sulhun ta Sudan Ta Kudu masu shiga tsakani na ganin akwai banbanci wannan karon.

https://p.dw.com/p/1EUQ2
Südsudan Waffenstillstand 01.02.2014 Addis Abeba
Hoto: Reuters/T. Negeri

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da madugun 'yan tawayen kasar Riek Machar sun amince da wata sabuwar yarjejeniyar tsagaita don kawo karshen rikicin da ke wakana tsakanin bangarorin biyu. Wannan dai ba shi ne karon farko da bangarorin biyu suka cimma irin wannan yarjejeniya ba, don a bara ma sun yi kwatankwacin haka amma kan tafiya tai nisa maganar ta lalace.

Yarjejeniyar ta yanzu dai ta tanadi girka gwamnatin wucin gadi tsakanin Kiir da Machar, batun da ka iya maida Machar din kan mukaminsa na mataimakin shugaban kasar, to sai dai masu sanya idanu kan lamarin Sudan ta Kudun din na gani da wuya a wannan karon ma daidaiton da aka samu ya dore.

Konflikt im Südsudan Regierungssoldaten 25.12.2013
Sojojin gwamnati na taimakwa wajen daidaita rikicinHoto: Samir Bol/AFP/Getty Images

Yarjejeniyar za ta dore a wannan karon

Firaministan Habasha kana shugaban kungiyar kasashen nan ta IGAD Hailemariam Dassalegn ya ce ya yi imanin komai zai daidaita: "Shugabannin biyu za su mutunta yarjejeniyar da suka sanyawa hannu. Wannan shi ne abinda al'ummar Sudan ta Kudu da kasashen yankin da ma sauran kasashen duniya baki daya muradin gani. Rashin yin aiki da yarjejeniya zai jawo naksu garemu baki daya musamman ma ga mahukuntan Sudan ta Kudu din."

Wannan tabbaci na nuna kwarin gwiwa kan yin aiki da yarjejeniyar da shugabannin biyu suka sanyawa hannu da ma kalamai irin na jan kunne a garesu na daga cikin abubuwa da suka sanya samun kwarin ga al'ummar Sudan ta Kudu. To sai dai wasunsu na cewar ba girin-girin ba ta yi mai domin kuwa, a baya sun ga irin wannan amma kuma daga bisani aka koma gidan 'yar jiya.

Friedensabkommen für den Süd-Sudan
'Yan kasa sun kosa a sami zaman lafiyaHoto: AP

Ba girin-girin ba ta yi mai

Masu shiga tsakani kan rikicin na kasar dai sun ce hanya daya ce tilo ta kaiwa ga dorewar zaman lafiya a wannan jaririyar kasa kuma itace ta kauarcewa nunawa juna 'yar yatsa. Seyoum Mesfin da ke zaman madugun masu shiga tsakani na kungiyar IGAD ta kasashen gabashin Afirka na da irin wannan tunani: "Dole ne bangarorin biyu su jingine batun na cewar hari suka kawo mana wanda ya sa muka maida martani saboda a halin da ake ciki babu wani dalili na kaiwa juna farmaki. Abinda ake bukata shi ne sahihiyar tsagaita wuta shi ne ake bukata a Sudan ta Kudu."

Yanzu haka dai kasashen nahiyar Afirka da ma na duniya baki daya sun sanya idanu don ganin yadda za ta kaya a kwanaki ko makonnin da ke tafe.