Yunkurin hana zaben raba gardama ga Kurdawan Iraki
September 22, 2017Mambobin Kwamitin ga baki daya sun nuna goyon bayansu ka kasancewar kasar Iraki kasa daya dunkulalliya, inda suka yi kira da a bi hanyoyin da kundin tsarin mulkin kasar ta Iraki ya tanada, wajen warware duk wani rikici tsakanin gwamnatin tsakiya da kuma ta jihar ta Kurdawa, tare da ganin ko wane bangare ya yi sassauci daga matsayinsa a karkashin kulawar kasa da kasa.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya bada goyon bayansa ga kokarin majalisar na shiga tsakani wajen samar da wani dandali na tattaunawa tsakanin bangarorin. Majalisar Dinkin Duniya dai ta sha alwashin cimma matsaya nan da zuwa shekaru uku masu zuwa, tsakanin gwamnatin ta Iraki da kuma ta jihar Kurdawan kasar, a kan makomar da ta dace da yankin Kurdawan na Iraki ta hanyar sulhu.