Yunkurin juyin mulki a Sudan ta Kudu
December 16, 2013Rikicin dai ya balle ne a wani barikin soja da ke dab da tsakiyar birnin na Juba, kafin daga bisani ya bazu zuwa sassa daban-daban na birnin. Shaidun gani da ido da sauran jakadun kasashen ketare sun bayyana cewa an yi amfani da manya-manyan bindigogi yayin fadan.
An dai ruwaito Shugaba Salva Kirr na kasar ta Sudan ta Kudu da ba ta dade da samun 'yancin kanta daga kasar Sudan ba, na danganta rikicin da wani yunkurin yi masa juyin mulki. Haka nan ma ya zargi tsohon mataimakinsa da ke zaman abokin adawarsa, Riek Machar, da ya kora daga mulki a kwanakin baya, da hannu a ciki. Ya kuma ce za a sanya dokar takaita zirga-zirga a birnin na Juba daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe