Kasar Kenya da ke fuskantar matsalar fari ta fada a cikin kasashen gabashin Afrika da a yanzu haka alkaluma suka nuna da cewa mutane akalla miliyan ashirin ke cikin matsala ta matsannaciyar yunwa, matsalar ta Kenya ta munana a sanadiyyar almundahana da rashawa da ta dabaibaiye kasar.