Yunƙurin daidaita Sudan da Sudan ta kudu
May 29, 2012Ƙasashen Sudan da kuma Sudan ta kudu sun koma kan teburin tattaunawa a birnin Addis Abeba na Habasha, da nufin warware taƙaddamar kan iyaka da ke hana ruwa gudu tsakanisu. Tsohon shugaban Afirka ta kudu Thabo Mbeki ne ya ke jagorantar tattaunawar zamana lafiyar da yawun ƙungiyar Gamayyar Afirka, tsakanin Idriss Mohammed Abdel Qadir da ke wakiltan Sudan da kuma Pagan Umum da ke magana da yawan Sudan ta kudu. Tun dai farkon watan afiliu ne fadar mulki ta Khartum ta fice daga zauren tattaunawar, sakamakon mamaye yankin Heiglig mai arzikin man fetur da Sudan ta kudu ta yi.
Babban batu da ganawar birnin Addis Abeba za ta sa a gaba, shi ne laluɓo hanyoyin warware taƙaddamar kan iyaka tsakanin maƙobtan biyu cikin ruwa sanyi. Tun bayan da Sudan ta kudu ta sami 'yancin cin gashin kanta a shekarar da ta gabata ne, dangantakar Sudan da kuma Sudan ta kudu ke daɗa tsami sakamakon rikicin kan iyaka. A makon da ya gabata ne sassa biyu suka amince su sake sulhunta gabar da ke tsakaninsu bayan da suka yi ta shan matsin lamba daga ƙungiyar Gamayyar afirka da kuma kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi