1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a bude harkokin kasuwanci a Amirka

April 16, 2020

Amirka ta bayyana aniyar sake bude harkokin da ta dakatar da nufin yaki da yaduwar annobar da duniya ke ciki, wadda ta fi muni a kasar a yanzu, bayan gamsuwa da aka yi.

https://p.dw.com/p/3ayrT
USA Corona-Pandemie | Trump Statement
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Brandon

Shugaba Donald Trump na Amirka zai bayyana shirin janye dokar hana fita da aka kafa a fadin kasar, daidai lokacin da wadanda cutar kashe da ma kamawa ke fin na ko wace kasar duniya. Akalla dai cutar ta kashe Amirkawa sama da dubu 2,500 a Larabar da ta gabata kadai, yayin da ake da sama da mutum dubu 28 suka mutu jumilla, sai kuma wadanda kuma ke fama da ita da suka zarta dubu 644.

Shugaba Trump ya yi bayanin cewa kasar ta wuce kololuwa a bangaren yaduwar wannan annoba a yanzu, koda yake ana kan yaki da ita babu kama hannun yaro. Tun da fari dai Jamus kasar da mace-mace sakamakon cutar ke kasa a nahiyar Turai da saurarn manyan kasashe ke kasa, ta bayyana wasu shirye-shiryen dawo da harkoki cikin kasarta sannu a hankali.