Za a ci gaba da zanga-zanga a Zimbabuwe
September 12, 2016'yan adawa a Zimbabuwe sun kuduri aniyar ci gaba da gudanar da zanga-zanga a duk fadin kasar. A karshen makon da ke tafe ne 'yan adawar ke shirin gudanar da gangamin kalubalantar hukumar zaben kasar a gabannin zabubbukan shekara ta 2018. Jam'iyyu 18 ne dai suka yi gamayyar kyamatar halayyan hukumar zaben da su ke ganin akwai nuna son kai da alamar marawa shugaban kasar Robert Mugabe baya.
To sai dai jam'iyun adawa a kasar na son yin amfani damar wannan zanga-zanga da nufin jan hankalin kasa da kasa da wakilan Majalisar Dinkin Duniya wajen sanya idanun a zaben kasar nan gaba. Wannan dai na zuwa ne makonnin kadan bayan da 'yan adawar su ka shirya wata zanga-zangar da ta rikede zuwa tashin hankali wanda ya yi jawo 'yan sanda suka yi ta fesa hayaki mai sa hawaye a kan masu zanga-zangar da suka mamaye Harare babban birnin kasar.