An zargi al-Bashir da laifin cin hanci da rashawa
June 13, 2019Wata sanarwa da masu shigar da kara suka fitar a wannan Alhamis ce ta tabbatar da hakan, inda a ciki aka nemi a soma tuhumar shugaban da matsin masu zanga-zanga ya kawo karshen mulkinsa na shekaru talatin. Sakamakon binciken dai, wanda aka soma gudanarwa ne tun bayan da aka hambarar da gwamnatinsa a watan Febrairun da ya gabata.
An dade ana neman a mika al-Bashir gaban kotun kasa da kasa ta ICC wacce da ma ta ba da sammacin kamo shi tun a shekara ta 2009 a bisa zargin aikata kisan kiyashi a yakin Darfur da kuma na baya-bayan nan, gano tarin daloli da aka yi a muhallinsa bayan da aka kai shi gidan yari a karshen mulkinsa.
Tsugune dai ba ta kare ba a Sudan kan rikicin samar da gwamnati, a yau ne aka soma wani zagayen ganawa a tsakanin jagoran mulkin soji na riko da wasu wakilai na Amirka da Afirka inda ake sa ran za su lalubo hanyar kawo karshen rikicin dama samar da sabuwar gwamnati.