Za a je zagaye na biyu a zaben Laberiya
December 7, 2017Talla
Babbar kotun koli a kasar Laberiya ta bayyana a wannan rana ta Alhamis cewa shedu da ta tattara game da zargin magudin zabe a zaben kasar da aka yi a watan Oktoba, ba su gamsar da kotu ba ta bada umarni a sake zaben kasar, abin da zai bude kofa a tafi zagaye na biyu tsakanin 'yan takara tsohon tauraroron wasan kwallon kafa George Weah da mataimakin shugabar kasa Joseph Boakai.
Mai shari'a Philip Banks da yake bayyana hukuncin kotun ya ce shedu da kotu ta tattara ba za su sanya a ce za a sake zaben bakin dayansa ba.