Za a kaddamar da Beiden da Harris a Amirka
August 17, 2020Duba da yadda matsalar annobar Covid-19 ke ci gaba da yin kamari, za a gudanar da zaben shugabancin kasar Amirka ne galibinsa ta hanyar kada kuri'a daga gidan waya, matakin da kuma tun kafin a je ko'ina, jam'iyyar Democrat ke zargin abokiyar hamayyarta ta Republican musamman ma shugaba Donald Trump mai shekarau 74, da yunkurin kawo tangarda ga tsarin gidan waya, a wani mataki na karkata sakamakon zaben, zargin da shugaban ya musanta yana mai bayyana bangaren Joe Beiden mai shgekaru 77 da neman assasa magudi.
Ko a yammacin jiya kakakin majalisar dokokin Amirka Nancy Pelosi, ta bayyana yunkurin kiran wani taron gaggawa na majalisar a wannan makon, a wani mataki na kafa doka da ka iya hana shugaba Donald Trump aiwatar da duk wasu sauye-sauye ga tsarin gidan wayar kasar.