Yiwuwar kafa sabuwar gwamnati a Sudan
October 29, 2021Talla
A wata hira da yayi da kamfanin dillancin labaru na Rasha Ria Novosti, jagoran kifar da mulkin ya ce nan ba da jimawa za a zabi gogaggen ma'aikacin gwamnati a matsayin sabon shugaban gwamnati, wanda zai nada majalisar zartarwar da za ta mulki kasar.
A ranar Litinin dinnan ce dai sojoji suka kifar da mulkin wannan kasa ta yankin gabashin Afirka, biyo bayan rikicin siyasar da ya mamaye Sudan din. Janar Al-Burhan ya sanar da rusa gwamnatin rikon kwaryar kasar tare da kafa dokar ta baci.
Juyin mulkin na zuwa ne bayan makonni na zanga zangar adawa da gwamnatin wucin gadi a karkashin jagorancin Abdalla Hamdok, da wasu rigingimu na siyasa a Sudan din mai yawan al'umma miliyan 44.