1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Za a kashe jami'in da ya taka mutum da mota

Abdul-raheem Hassan
May 24, 2021

Wata kotu a Sudan ta yanke hukuncin kisa kan wani mai kan sarki bayan samun sa da laifin kashe wani mai zanga-zanga lokacin juyin juya halin kasar shekaru biyu da suka gabata.

https://p.dw.com/p/3tsRn
Hammer Gerichtssaal Gericht Richter-Hammer
Hoto: Adrian Wyld/empics/picture alliance

Kotun ta ce Youssef Mohieldin al-Fiky ya taka daya daga cikin masu bore da mota har lahira yayin tarwatsa dandazon zanga-zanga da aka yi a birnin Khartoum a 2019.

Marigayin Hanafy Abdel-Shakour yana cikin mutane sama da 120 da ake zargin jami'an tsaron gwamnati suka kashe lokacin zaman dirshen a wajen hedikwatar sojojin Sudan a boren bayan hambarar da gwamnatin tsohon Shugaban kasar Omar al-Bashir.