Za a yanke wa Hessene Habre hukunci
May 30, 2016Mai shekaru 73 da haihuwa , Hissene Habre ya shugabanci kasar ta Chadi daga shekara ta 1982 zuwa1990. A a tsawon wannan lokaci an zarge shi da tabka laifuffuka da suka saba wa bil Adama da azabtarwa. Masu shigar da kara na neman a yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan kaso.
Tun daga watan Juli ne dai Habre yake gaban kotun ta musamman da Kungiyar Gamayyar Afirka ta kafa a birnin Dakar, bisa ga yarjejeniya da gwamnatin kasar ta Senegal.
Hukuncin na tsohon shugaban kama karya na kasar Chadi na zaman irinsa na farko da wata kasa za ta yi wa wani tsohon shugaban kasa bisa laifuffuka da ya aikata a lokacin da yake kan karagar mulki.
Reed Brody da ke zama lauyan kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Human Rights Watch, wanda ya kwashe shekaru 15 yana binciken wadanda Habre ya ci zarafinsu, ya ce wannan zai taimaka wajen karfafa gwiwar irin wadannan mutane da aka zalunta gabatar da kokensu gaban hukuma.