1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a yi nazarin halin tsaro a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
June 28, 2017

Hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da rahoton da ke nuna yadda yanayin tsaro ke ciki a Tillabery da ke Tahoua da ke arewa maso yammacin Jamhuriyar Nijar mai makwabtaka da Mali.

https://p.dw.com/p/2fZXu
Nigeria Armee Task Force gegen Islamisten Boko Haram
Dakarun tabbatar da tsaro a Jamhuriyar NijarHoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Hukumar ta ce fiye da Asibitoci 10 ne aka rufe baya ga wasu tarin kasuwanni da jama'a ke hada-hadarsu a yankin sakamakon dokar ta-baci da yankin na Tillabery ke ciki. Rahoton na hukumar dai ya ambaci halin da jama'a suke ciki musamman ma a wasu jihohi 8 da ke makwabtaka da Mali a yankunan Tahoua da Tillabery wadanda walau ko suna makwabtaka ta kut-da-kut ko kuwa ba sa da nisa da yankin Mali inda ‘yan ta'adda ke fitowa daga yankin don kai hare-hare. Rahoton ya ce yanzu hakan hukumomin Nijar sun kai ga rufe iyakar kasar da Mali a mashigar jahar Abala baya ga wasu kasuwanni 16 da gwamnatin kasar ta rufe, da gwamnatin ke zargin ‘yan ta'addan ne da amfani da kasuwannin wajen sayen kayayyakin abinci da man fetur ko gami da magungunna. 

Niger Bevölkerungswachstum Frau mit Kindern
Mata da yara da rashin asibitoci ke shafaHoto: Getty Images/AFP/O. Omirin

Ko baya ga hakan ma, matakin inji rahoton ya kai ga rufe wasu asibitoci 11, gwamnatin ta rufe su don kubutar da su daga matsala. Ko da yake ra'ayi sun bambanta dangance da matsalolin da ke addabar jama'a a yankin duba da dokar ta-bacin da jihohin ke fuskanta ganin cewa tun fil azal, yankuna ne da ke fama da matsalolin karancin cimaka da rashin ingantacciyar rayuwa ga kuma tsananin fatara da jama'a ke ciki a yankin

Flüchtlingsfamilie aus Nigeria bei Diffa Niger
Wasu da rigimar tsaro ta raba da sukuniHoto: DW/Larwana Malam Hami

Yayin wata hira da tashar DW ta yi da shi, ministan tsaron Nijer Malam Kalla Moutary ya tabbatar da soma aiki da dokar ta-bacin gadan-gadan, inda ya ce sojojin kasar na aiki da ita kuma suna samun nasarori sannu a hankali inda suke kona duk wata mota ko gida ko wani abin hawa da suka lura ana aiki da su don cimma wani buri na ta'addanci. Ministan ya kuma yi kiran da a ci gaba da samun hadin kan jama'a don samun kwanciyar hankali mai dorewa a yankin da ke makwabtaka da kasar ta Mali.