Zabe a Tanzaniya
October 26, 2005Har dai ya zuwa halin da muke ciki yanzun ana ci gaba da gwagwarmaya mai tsananin gaske a yakin neman zaben kasar ta Tanzaniya, inda jami’an siyasa ke alkawarin ceto kasar daga matsalar talaucin da ta kai mata iya wuya da kuma yaki da cin hanci tare da daga matsayin mata. Akwai mace daya a tsakanin ‚yan takara goma dake gwagwarmayar neman mukamin shugaban kasa domin mayewa gurbin shugaba Benjamin Mkapa mai barin gado, wanda kuma daftarin tsarin mulkin kasar ya hana masa sake shuiga takarar zaben karo na uku. Kuma ko da yake ba za a iya hasashen dan takarar da zai lashe zaben ba, amma manazarta na sun yi imanin cewar dan takarar jam’iyyar dake mulki Jakaya Kikwete, shi ne zai yi nasara. Sai dai kuma a daya bangaren a kokarinsu na ganin sun samu nasara wasu ‚yan kananan jam’iyyun hamayya su biyar sun hade karkashin tuta guda suka kuma nada Edmund Mvungi, mai fafutukar kare hakkin dan-Adam, a matsayin dan takara bai daya tsakaninsu. Tsarin mulkin demokradiyyar a kasar Tanzaniya zai fuskanci babban kalubale a Zanzibar. Domin kuwa tun bayan zabubbukan da aka gudanar a lardin a shekara ta 1995 da kuma ta 2000 yankin ya zama wani dandalin gwagwarmayar neman madafun mulki, inda aka rika fuskantar tashe-tashen hankula jefi-jefi tsakanin magoya bayan jam’iyyar gwamnati ta Chama cha Mapinduzi da kuma na ‚yar adawa da Civic United Front. Shi kansa zaben lardin da aka gudanar a shekara ta 2000 sai da yayi sanadiyyar rayukan mutane sama da 40 sakamakon tashe-tashen hankulan da aka fuskanta bisa zargin magudin da su kansu masu sa ido daga kasashen ketare suka hakikance da shi. Kuma ko da yake jam’iyyun siyasar guda biyu sun sanya hannu akan wata yarjejeniyar dakatar da matakan ta da zaune tsaye, amma fa ga alamu tuni aka shiga zaman dardar dangane da zaben na ranar 30 ga wata. An ji wa mutane masu tarin yawa rauni sakamakon wani fadan da ya barke tare da amfani da adduna da kulake da kuma duwatsu. A halin yanzu haka kasashe da dama abin da ya hada har da Amurka sun gargadi ‚ya’yansu a game da kai ziyara kasar Tanzaniya har sai bayan an kammala zaben baki daya. Wani abin da jami’an siyasar kasar ta Tanzaniya hade da manazarta al’amuran yau da kullum suka yi imanin cewar zai taimaka wajen lafar da kurar rikicin siyasar, musamman a lardin Zanzibar shi ne idan dukkan jam’iyyun siyasar da lamarin ya shafe su, suka amince da kafa wata gwamnati ta hadin gambiza tsakaninsu. A yanzun dai sai kawai a dakata a saurari sakamakon zaben da kuma irin abin da zai biyo baya.