Zaben Amirka na iya yin tasiri kan kungiyar NATO
November 7, 2016Yayin da wa'adin shekaru 8 na mulkin shugaba Barack Obama na Amirka ke kawo karshe inda ake zaben sabon shugaban kasa, manufofin Amirka a kasashen dunyia na cikin abubuwan da duk wanda ya lashe zabe zai mayar da hankali a kai. Shugaba Obama ya bayar da fifiko ga kasashen Asiya, amma manufar shugaban ta samun yarjejeniyar kasuwanci da kasashen ta na ci gaba da samun tarnaki.
Duk dai wanda ya samu nasara tsakanin manyan 'yan takara biyu a zaben Amirka Donald Trump ko Hillary Clinton na da aiki kan yadda dangantaka tsakanin kasar ta Amirka za ta kasance da sauran kasashe musamman kan abubuwa masu sarkakiya da ake samun sabani cewar Erica Chenoweth da ke jami'ar Denver a Amirka masaniyar harkokin tsaron kasashen duniya
" Ya dace Tarayyar Turai ta zama abu na farko da duk wanda ya zama shugaban Amirka zai mayar da hankali, saboda Turai ta fi zama mafi muhimmanci a kawancen Amirka."
Sai dai Chenoweth ta kara da cewa akwai wasu wuraren da za a mayar da hankalin irin Siriya, da yaki da ta'addanci, da batun nukiliyar Iran, da sanin hanyoyin tafiyar da dangantaka da China, da sauyin yanayi gami da dakile masu kaifin kishin kasa da suke samun tagomashi.
A daya bangaren James Jay Carafano masanin tsaro na gidauniyar Heritage ya ce tilas ne sabon shugaban na Amirka ya tinkari Rasha:da batun zaman lafiya da tsaro.
Dukkan masanan biyu sun amince cewa ya dace Amirka ta karfafa dangantaka da kasashen Turai, domin hakan zai taimaka wajen magance matsaloli da dama da ake samu tsakanin kasashen duniya. Kungiyar tsaro ta NATO-OTAN ta na taka muhimmiyar rawa kan tsaro da zaman lafiya kuma karfafa kungiyar zai taimaki kasashen na Turai da Amirka. Sai dai Erica Chenoweth na jami'ar Denver da ke Amirka ta na ganin ya dace kungiyar ta koma kan manufofin da aka kafa ta akan su, musamman idan aka dubi abin da ya faru a Libiya:
"Ina tsammani manufar kungiyar tsaro ta NATO/OTAN kan Libiya da wasu wurare an samu akasi domin sun karkata daga aikin su, saboda haka dole kungiyar tsaron NATO ta koma kan hanyar da aka gina ta a kai na yarjejeniyar kare juna tsakanin kasashen da suke nahiyoyin da ke ciki."
Yanzu dai abin jira a gani shi ne kalubalen da duk wanda zai lashe zaben tsakanin Donald Trump da Hillary Clinton zai fuskanta.