1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Amurka na 2024: Amurkawa na kada kuri'a

November 5, 2024

Milyoyin Amerikawa na cigaba da yin dandazo a rumfunan zabe domin kada kuri'unsu duk da yake yau ba ranar hutu ba ce ga ma'aikata, amma an rufe makarantu domin yin amfani da su a matsayin cibiyoyin zabe.

https://p.dw.com/p/4mexz
US-Wahl 2024 | Stimmabgabe JD Vance in Cincinnati
Hoto: Stephen Maturen/Getty Images

Mai yiwuwa karuwar sabbin matasa masu yin zabe a karon farko da kuma Amurkawa masu maganar da harshen sipaniyanci da ake kira Latino su fiye da milyan 30 da suka cancanci yin zabe a bana, su raba gardama wajen fiddo da sabon shugaban kasa a tsakanin Donald Trump na Republican da Kamala Harris ta Demokrats.

Karin Bayani: Tasirin da sakamakon zaben Amurka ga kasar Jamus

Alal misali, bisa wata kididdiga ta jami'ar California, UCLA, a Pennslvania kadai, jiha mai matukar mahimmanci, akwai 'yan Latino  kusan dubu 600 masu rajistar yin zabe.

Karin Bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka

Donald Trump da mai dakainsa Melania
Donald Trump da mai dakainsa MelaniaHoto: Evan Vucci/AP/picture alliance

A wasu runfunan zabe da ke yankin Washington da kuma jihar Maryland masu kada kuri'a sun baiyana ra'ayoyi mabambanta. Wata mata mai suna Linda ta ce, ta gaji da yadda Donald Trump yake mayar da mata saniyar ware a Amurka. Yayin da Mustapha Muhammad daya daga cikin Amurikawa 'yan asalin Afrika ya ce yana goyon bayan Trump saboda yadda jam'iyyarsa ta Republican ta tafi da tsarin dimukuradiyya.

Karin Bayani: Me zaben Amurka ke nufi ga Afirka?

An tsaurara matakan tsaro a gidan Shugaban kasa da mataimakiyarsa Kamala, inda a wasu  jihohi 27 kuma, ma'aikatar shari'a ta tura jami'an sa idanu bayan na tsaro, a wasu kuma, aka sa shamaki da gilashin da harsashe ba zai iya hudawa ba, a tsakanin ma'aikatan zabe da masu kada kuri'a.

Kamala Harris
Kamala Harris Hoto: David Swanson/REUTERS

Farfesa Aisha Ali Gombe, Malamar koyar da ilimin alkinta bayanai a na'ura mai kwakwalwa da ke Jami'ar jijar Lousiana, ta na kallon lamarin zaben daga yadda kasashe irinsu Rasha da China ko kuma Iran, za su iya yin amfani da fasaha don kawo rudani a zaben na Amurika.

Karin Bayani: Kalubalen da ke gaban Kamala a Amurka

Baturen zabe Donald Benson da ke jihar Maryland cewa ya yi har yanzu ba su ga wata matsala ba.