Jam'iya mai mulki na kan gaba a Angola
August 25, 2022Talla
Hukumar Zabe ta nunar da cewa jam'iyya mai mulki ta MPLA din na kan gaba ne da sama da 52 cikin 100 na kuri'un da aka rigaya aka kidaya, yayin da jam'iyyar adawa ta UNITA ke biye mata da sama da kaso 42 cikin 100. Kawo yanzu dai an kidaya sama da kaso 86 cikin 100 na kuri'un da aka kada, inda a Luanda babban birnin kasar cikin kuri'u kaso 77 da aka kidaya jam'iyyar adawa ta UNITA ke kan gaba da kaso 62 cikin 100 kana MPLA mai mulki ke da sama da kaso 33 kacal. Shugaba Joao Lourenco na Angolan na neman wa'adi na biyu, inda yake fafatawa tare da abokin adawarsa na jam'iyyar UNITA Adalberto Costa Junior a zabe mafi rikici da Afirka ta shaidar cikin tsawon shekaru.