1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Angola

Zainab A MohammedAugust 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5k

Hadin gwiwar jammiyyun adawa guda 20 a Angola,sun bayyana damuwansu dangane da rashin ingantaccen shiri,dangane da gudanar da zaben kasar na farko ,bayan yakin basasar shekaru 4 .

Shugaba Jose Eduardo dos Santos,wanda ke jan ragamar mulkin kasar tun daga 1979,yayi alkawarin gudanar da zaben kasa baki daya ,kafin karshen shekara mai gabatowa,to sai dai kungiyoyin jamaa dana jammiyyun adawa na ganin cewa har yanzu babu wani shiri da hukumar zaben kasar tayi dangane da wannan zabe.

A sanarwar hadin gwiwa da suka gabatar ayau,jammiyyun adawan sun bayyana damuwansu dangane da tafiyar hawainiya da hukumar zaben keyi dangane da shirye shiryen gudanar da wannan zabe.Bugu da kari sanarwa ta bukaci hukumar zaben Angolan data kira taro da jammiyyun adawan kasar a mako mai zuwa ,domin gabatar musu da shirin da akayi dangane da batun kada kuriu