1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben kasar Kenya ya mamaye jaridun Jamus

August 12, 2017

A wannan makon jaridun Jamus sun fi mayar da hankali kan zaben shugaban kasar Kenya da ya gudana a ranar Talata.

https://p.dw.com/p/2i49f
Kenia Mombasa Präsidentschafts- und Parlamentswahl
Hoto: Getty Images/AFP/T. Jones

A sharhin da ta rubuta kan zaben Kenya, jaridar Süddeutsche Zeitung ta fara ne da cewa Kenya a cikin yanayi na shakku sannan sai ta ci gaba da cewa a shekarun baya ana daukar kwanaki masu yawa kafin a kammala kidayar kuri'u na zaben shugaban kasa a Kenya amma awoyi kalilan bayan zaben na ranar Talata, dan takarar 'yan adawa Raila Odinga ya ce an tabka magudi a zaben, inda ya kira sakamakon farkon da aka samu da cewa abin kunya ne da ba za a iya yarda da shi ba. Matakin kin amincewa da sakamakon zaben dai ya tuna wa 'yan Kenya mummunan rikicin nan da ya biyo bayan zaben 2007 inda aka kashe mutane fiye da dubu daya.Dama tun gabanin a gudanar da zaben Odinga ya ce zai amince da sakamako ne idan shi ne ya yi nasara.Ita ma a tsokacin da ta yi game da zaben na kasar Kenya jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa ta yi ana zargin tabka magudi a zaben shugaban kasar Kenya. Ta ce yayin da magoya bayan shugaba mai ci Uhuru Kenyatta suka bayyana sakamakon wucin gadi na zaben da wani abin farin ciki, shi kuwa bangaren 'yan adawa karkashin jagorancin Raila Odinga watsi suka yi da sakamakon da cewa an yi kutse a na'urar tattara sakamakon zabe na hukumar zaben kasar.

Jacob Zuma ya tsallake rijiya da baya

Südafrika Präsident Zuma übersteht erneut Misstrauensantrag
Hoto: Reuters/M. Hutchings

Daga zaben shugaban kasar Kenya sai kuri'ar neman tsige shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma da majalisar dokokin kasar ta yi. A sharhin da ta yi dangane da wannan batu, jaridar Die Tageszeitung ta fara ne da cewa Shugaba Jacob Zuma ya sake tsallake rijiya da baya a kuri'ar rashin amincewa da shi inda 'yan majalisa 177 suka kada kuri'ar amincewa da neman tsige shugaban da 'yan adawa suka gabatar, yayin da 198 suka yi watsi da shirin. Jaridar ta ce ko da yake zaben bai zo da mamaki ba, amma a wannan karo an samu canji mai muhimmanci inda da yawa daga cikin 'ya'yan jam'iyyar ANC suka kada kuri'ar yankan kauna ga shugaba Zuma. Haka dai ya yiwu ne saboda a karon farko an kada kuri'ar ce a asirce. Da yawa daga cikin masharhanta na masu ra'ayin cewa maimakon karfafa ikon Shugaba Zuma, wannan kuri'ar ta kara tsananta rikicin da ke cikin jam'iyyar ta ANC ne.

Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango

Demokratische Republik Kongo Polizei
Hoto: Getty Images/AFP/M. Mulopwe

Idan muka leka kasar jamhuriyar demokuradiyyar Kwango kuwa har wayau jaridar ta Die Tageszeitung ce ta yi tsokaci kan yajin aikin gama gari na kwanaki biyu da 'yan adawar kasar suka kira a wannan mako. A labarin da ta yi wa taken "Yakin neman goyon bayan jama'a" jaridar ta ce dab da fara yajin aikin a ranar Talata, gwamnatin Shugaba Joseph Kabila ta katse hanyoyin sadarwa na Intanet. Amma duk da haka 'yan adawa sun wallafa hotuna a kafafan sada zumunta, da ke nuna tituna sun kasance wayam, wato an amsa kiran shiga yajin aiki. Amma daga nata bangaren gwamnati ta ce kasuwanni sun cika makel da jama'a.