Zaben Kenya ya bar baya da kura
August 13, 2017Talla
'Yan adawa na kasar Kenya sun sha alwashin ci gaba da nuna tirjiya ga sakamakon zaben da ya sake bai wa Shugaba Uhuru Kenyatta nasara, tare da kawar da yuwuwar zuwa kotu, saboda gwamnati ta karya lagon alkalai. An samu tashe-tashen hankula a wasu wurare da ke zama tungar jagoran 'yan adawa Raila Odinga wanda ya zo na biyu a zaben. Hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar ta mutane 24 suka hallaka sannan kusan 100 suka samu raunika tun bayan gudanar da zaben na ranar Talata.
Ana ci gaba da zaman tankiya bisa matakin 'yan adawa na fatali da sakamakon zaben. Sai dai kawo yanzu babu alamu za a sake makamancin rikicin da ya biyo bayan zaben shekara ta 2007, lamarin da ya kai ga mutuwar fiye da mutane 1000 yayin da wasu da dama suka smau raunika.