Kenya ta yi sabon shugaban kasa
August 19, 2022Kasar Kenya an sanar da sakamakon zaben shugaban kasa, inda jaridar Süddeutsche Zeitung ta yi labarin ta ce kalmar Ingilishi ta "Hustler" ko zafin nema, yanzu ta shahara a Kenya, kuma hakan ya biyo bayan hazikin mutum mai shekaru 55 da haihuwa daga tsaunukan Kenya: William Ruto. Ya yi amfani da kalmar a yakin neman zabensa. Ruto ya kira Kenya a matsayin "kasa mai cin hanci." Kuma a yanzu yana son ya jagorance su zuwa kyakkyawar makoma bayan da aka ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar. Ko da shike ba zai iya tabbatar da nasararsa ba tukuna, saboda abokin hamayyarsa Raila Odinga yana jin an ci amanarsa kuma yana son ya kalubalanci sakamakon a kotu.
Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung batun takaddamar Mali da kasashen Yamma ta yi wa sharhi. Jarida ta fara da cewa wani jirgin sama ya sauka a Mali wanda Bundeswehr wato rundunar sojan Jamus za ta iya musanya sojoji da shi. Amma akwai shakku game da amfani da shi. Jirgin saman ya tashi daga birnin Kolon da zummar zuwa Mali domin a sauya wasu sojojin Jamus su dawo gida don hutawa wasu kuma su maye gurbinsu, amma kwazam sai aka ji labarin cewa ba tabbas ko jirgin zai iya samun nasarrar sauka. Masu rike da madafun iko a Mali dai sun shafe kusan wata guda suna hana zirga-zirgar jiragen sama daga tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta MINUSMA. Wannan kuma ya shafi samar da jiragen sama da sojojin ke bukata don aiki.
Ziyarar Sakataren harkokin wajen Amirka wasu kasashen Afirka. Labarin wanda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi ya fara ne da haka. Ayyukan daidaita tsakani da Antony Blinken ya yi. Wato dai Sakataren na harkokin wajen Amirka ya yi jawabi kan wasu muhimman batutuwa a kasar Ruwanda. Halin da ake ciki a gabashin Kongo yana daya daga ciki. Abu na karshe a ziyararsa ta Afirka shi ne Antony Blinken ya jawo hankalin kasashen bisa sassautawa. Bayan ya isa kasar Rwanda, ya zanta da shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame da ministan harkokin wajen kasar Vincent Biruta game da tashe-tashen hankula da ke faruwa a yankin iyakar Kongo da Ruwanda. Blinken ya ce an tattauna hanyoyin rage zaman dar-dar a tsakanin kasashen biyu. Gwamnatocin Amirka da na Ruwanda sun dade suna kawancen kut-da-kut. Kafin ziyarar zuwa Ruwanda, Blinken ya nuna matukar damuwa a Kongo game da abin da ya bayyana a matsayin rahoton Majalisar Dinkin Duniya, cewar akwai shaidun da ke nuna Ruwanda ta goyi bayan wata fitacciyar kungiyar 'yan tawaye mai suna M23 a gabashin Kongo. Gwamnatin Rwanda ta musanta rahoton.