Zaben majalisar dokoki a kasar Angola
August 31, 2012A wani abu da ba'a saba gani ba birnin Luanda babban birnin kasar ta Angola ya kasance shiru yayin da aka bada hutu a fadin kasar domin baiwa jama'ar kasar wadanda suka cancanci kada kuri'a su kimanin miliyan tara da dubu dari bakwai damar kada kuri'unsu a mazabu fiye da 10,000 da aka tanadar a makarantu a ko ina a fadin kasar.
Ko da yake kada kuri'ar baya tafiya da sauri kamar yadda jama'a suka bukata amma an sami gagarumin cigaba idan aka kwatanta da zabukkan baya na shekarar 2008 inda aka tsawaita zaben har izuwa rana ta biyu saboda hargitsi da aka samu rumfunan zabe. Shugaban hukumar zaben Andre da Silva Neto ya bayani da cewa "An samar da dukkan abin da ake bukata na kayan aiki da kuma turawan zabe domin gudanar da zabbukan cikin nasara ba tare da wata tangarda ba.
Shugaban hukumar zaben Andre da Silva Neto yace ana sa ran samun sakamakon zaben a Asabar. Wannan dai shine zabe karo na uku tun bayan da kasar ta Angola ta sami mulkin kai a shekarar 1975 daga kasar Portugal wadda ta yi mata mulkin mallaka.
Tun farko jam'iyyar adawa ta Unita ta baiyana fargaba cewa za'a kori yaynta daga rumfunan zabe saboda matsalolin dake tattare da jadawalin masu kada kuri'a, yayin da a waje guda kuma ta yi korafin cewa ba dukkan wakilanta masu sa ido bane aka bari suka shiga cibiyoyin da ake gudanar da zaben kamar yadda shugaban Jam'iyyar ta UNITA kuma dan takararta na shugaban kasar Isaias Samakuva ya nunar " Wannan zabe baki dayansa yana tattare da matsaloli amma duk da haka mun yanke shawarar shiga a dama da mu. Za mu yi hakan kuwa cikin martaba da kamala".
Babu tantama cewa shugaba Dos Santos wanda ya shafe shekaru 33 yana mulkin kasar zai sake yin tazarce na wasu shekaru biyar a karagar mulki. A zaben shekarar 2008 Jam'iyyarsa ta MPLA ta sami kashi 80 cikin dari na kuri'un da aka kada. Dos Santos shine shugaba na biyu a Afrika wanda ya fi dadewa a karagar mulki bayan shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo.
Gabanin fara zaben a yau shugaban hukumar zaben ta Angola Andre da Silva Neto ya bukaci jama'a su bada cikakken hadin kai domin gudanar da zaben cikin nasara " Ina kira ga masu kada kuri'a su kasance cikin nutsuwa su nuna da'a da hakuri da sanin ya kamata"
Da yake jawabi baayan kada kuri'arsa a mazabar dake wata marakanta kusa da fadar shugaban kasa, shugaba Dos Santos yace ya gamsu da yadda al'amura ke gudana cikin tsanakia ko ina a fadin kasar.
Shi dai shugaba Dos Santos ya yi amfani da tsawon shekarun da yayi a karagar mulki wajen karfafa madafan iko a hannunsa. Iyalinsa musamman ma 'yarsa Isabel ita ma ta kankane harkokin mai na kasar Angola inda ta shimfida wata daular kasuwanci.
A waje guda dai manazarta na ganin shugaba Dos Santos ya yi rawar gani inda ya zuba makudan kudade wajen sake gina kasar wadda ta shafe shekaru 41 tana fama da yake-yake wanda ya hada da shekaru 14 da aka kwashe ana gwagwarmayar neman yanci da kuma shekaru 27 na yakin basasa. Tsawon shekaru goma ya zuwa yanzu tattalin arzikin kasar na daga cikin mafi bunkasa a duniya.
Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi