Zaben Senegal: An fidda sakamakon karshe
August 5, 2017Talla
Gamayyar jam'iyyun da ke goyon bayan tsohon shugaban kasar Abdoulaye Wade, su kuma sun samu kujeru 19 sannan gamayyar jam'iyyu da ke goyon bayan magajin garin birnin Dakar Khalifa Sall da ke tsare a gidan kaso su kuma sun samu kujeru bakwai. Sai dai wannan sakamako da hukumar zaben kasar ta Senegal ta bayar zai samu amincewar kotun tsarin mulkin kasar ne kafin ya kasance na dindindin. Tuni bangaran Khalifa Sall ya yi watsi da wannan sakamakon. Tun dai daga ranar Litinin da ta gabata ne bangaran masu mulkin suka yi shelar lashe zaben, inda suka ce sun yi nasara a jihohi 42 daga cikin jihohi 45 na kasar.