1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirye-shiryen zabe a Cote d'Ivoire da Tanzaniya

Suleiman Babayo / LMJOctober 22, 2015

Ranar Lahadi 25 ga watan Oktoba al'ummar kasar Cote d'Ivoire za su zabi sabon shugaban kasa. Su ma dai na Tanzaniya a wannan rana ce suke nasu zaben, kana akwai zaben jin ra'ayin jama'a a Congo Brazaville.

https://p.dw.com/p/1GsdL
Alassane Ouattara shugaban kasar Cote d'Ivoire
Alassane Ouattara shugaban kasar Cote d'IvoireHoto: AFP/Getty Images/I. Sanogo

Shugaba Alassan Ouattara ya na kasar Cote d'Ivoire dai na da kyakkyawar damar sake lashe zaben saboda yadda aka samu bunkasar tattalin arziki. Wani fanni mai muhimmanci shi ne zaman lafiya da sasanta al'umar kasar ta Cote d'Ivoire.da ya samu nasarar yi. Kwanaki kalilan suka rage kafin zaben na ranar 25 ga watan Oktoba kuma ana ci gaba da gangamin neman Ouattara da suke wa lakabi da ADO ya samu kuri'u. Mariame Souare tana cikin magoya bayan Shugaba Ouattara ta kuma ce:

"Ni ce Mariame Souare. Muna tare da ADO. Bugu daya za mu yi, shi ne shugaban Cote 'Ivoire. Shi mutum ne da yake tsayuwa kan maganarsa, kan abin da ya fada. Muna bayansa, mun yarda da shi."

Karfin gwiwa da rashin yadda

Masu ra'ayin Shugaba Ouattara suna da karfin gwiwa. Amma akwai rashin yarda tsakanin yankin Arewaci da Kudancin kasar. Mariame Souare tana ganin maganar rarrabuwa tsakanin kudu da arewaci ya zama tarihi:

Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da ake zargi da tayar da tarzoma a 2010
Tsohon shugaban Cote d'Ivoire Laurent Gbagbo da ake zargi da tayar da tarzoma a 2010Hoto: AP

"A'a babu komai. yanzu duk abun da ya rage shi ne kawai zaman lafiya babu wani kace-nace. Abin da muke bukata ke nan."

Ta kara da cewa ita ta fito daga Arewaci kuma tana rayuwa babu wata matsala a yankin kudanci. An samu rarrabuwa tsakanin arewaci da kudancin kasar ta Cote d'Ivoire lokacin zaben shekara ta 2010, abin da ya zama babbar matsala. Tsakanin Ouattara da shugaban Laurent Gbagbo na wancan lokaci babu wanda ya samu gagarumar nasara. Sai da aka tafi zagaye na biyu inda Gbagbo ya ki amincewa da shan kayi. Haka ya jefa kasar cikin yaki na wasu watanni da shugabanni biyu da raba sojoji gida biyu gami da gwamnatoci biyu.

Mutane sun hallaka a zaben 2010

Bayan shigar dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da sojojin Faransa an cafke Gbagbo a watan Afrilu na shekara ta 2011. A gaba daya kimanin mutane 3000 suka hallaka. Pascal Affi N'Guessan na jam'iyyar Gbagbo ta FPI ya kasance tsohon Firaminista kana yana cikin masu neman shugabancin kasar a zaben da ke tafe:

"Akwai 'yan Arewa da suke Kudu, akwai 'yan kudu da suke arewa. 'Yan Cote d'Ivoire sun saba rayuwa tare. A wani lokaci an samun zaman zullumi. Amma yanzu muna cikin wani yanayi na sasantawa da juna."

Rikicin bayan zaben 2010 da ya haddasa asarar rayuka masu yawa
Rikicin bayan zaben 2010 da ya haddasa asarar rayuka masu yawaHoto: AP

Babbar tambayar ita ce makomar kasar ta Cote d'Voire da ke yankin yammacin Afirka, kamar yadda Martin Johr shugaban gidauniyar Friedrich Ebert da ke birnin Abidjan ke cewa:

"A ra'yina abu na farko shi ne tambaya kan sasantawa, da tambaya kan hukunta wadanda suka aikata laifuka, da wadanda suka tayar da husuma. Ina dandalin sasantawa? Shin ina makomar kasar? Kawo yanzu akwai rashin yarda tsakanin bangarorin al'umar kasar."

Shi ma Shugaba Alassane Ouattara a wannan mako ya yi alkawarin bai wa batun sasanta rikicin mahimmanci wajen gyara ga kundin tsarin mulki domin magance matsalolin. A yanzu dai 'yan takara takwas ne ke neman tsayawa takarar shugabancin kasar ta Cote d'Ivoire.