Zaben shugaban kasa a senegal
February 26, 2012Al'umar kasar Senegal ta hito da himma domin zaben shugaban kasa tsaknain 'yan takara 14.
Fiye da mutane miliyan biyar ne ta kamata su hito a yau, domin kada kuri'a, saidai zaben ya gudana a yayin da kasar ta shiga wata kwamacalar siyasa tsakanin 'yan adawa da shugaban kasa Abdullahi Wade.
Sabanin yadda aka yi hasashe, zaben ya gudana lami lafiya, kamar yadda Babu Diallo wakilin sashen faransanci na DW a birnin Dakar ya bayyana:Zabe ya wakana lau lami ,babu zanga-zanga, mutane sun fito sun kada dogayen layika domin kada kuri'unsu.A jimilice babu matsaloli masu tada hankali.
A yanzu hankulan al'umar kasar sun fara karkata ga hukumar zabe mai zaman kanta, wadda ke tattara sakamako.Tuni 'yan adawa sun zargi Hukumar zaben da zama kariyar farautar dan takara Abdullahi Wade.An yi wannan zabe tare da halartar masu sa ido daga ciki da wajen Senegal.
Mawallafi: Yahouza Sadissou
Edita: Usman Shehu Usman