1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben shugaban kasa a Senegal

March 25, 2012

Al'umar Senegal na kada kuri'a salin -alin domin tantance shugaban kasa tsakanin Wade da Sall

https://p.dw.com/p/14Rv7
Opposition presidential candidate and former prime minister Macky Sall addresses journalists during a press conference at a hotel in Dakar, Senegal Wednesday, Feb. 29, 2012. Leading Senegalese opposition candidate Macky Sall said Wednesday that if he wins a presidential runoff next month he will revise the constitution to reduce the presidential term from seven to five years and that he will apply the shorter term to himself, as well as the two-term limit that is already present in the constitution.(Foto:Rebecca Blackwell/AP/dapd) Senegalese President Abdoulaye Wade addresses journalists during a press conference at the presidential palace in Dakar, Senegal Monday, Feb. 27, 2012. As votes were being tallied on Monday from Senegal's Sunday presidential election, leading opposition candidate Macky Sall declared that no candidate had gotten the necessary 50 percent, making a runoff "inevitable." (Foto:Rebecca Blackwell/AP/dapd)
Macky Sall da Abdoulaye WadeHoto: dapd

Al'umar Senegal na cigaba da zaben shugaban kasa zagaye na biyu, inda ake fafatawa tsakanin shugaba mai barin gado Abdulahi Wade mai shekaru kusan 86 a duniya,da tsofan Firaministansa Macky Sall, wanda ya samu kashi 26 cikin dari a zagayen farko.

Ya zuwa wannan lokaci rahotanin sun tabatar da zaben na wakana lami lafiya,kuma kayan aiki sun wadata kamar yadda Demba Seydi shugaban wata runfar zabe ya bayyanawa Babu Diallo,wakilin sashen Faransanci na DW a Dakar babban birnin Senegal:Ya ce an kawo duk kayan zabe da ta kamata, akwatina, runfuna,takardu, da dai sauransu, sannan jami'an tsaro na bi sau da kafa domin ganin komi ya gudana ba tare da hargisti ba.

Zagayen farko ma ya wakana lami lafiya, saidai zullumin da jama'a ke hange shine,abinda zai biyo bayan bayyana sakamakon zagaye na biyu na zaben .

Baki daya 'yan takara 12 da ba su yi nasara kaiwa ga zagaye na biyu ba, sun umurci magoya bayansu su zabi Macy Sall, abinda masu kula da harakokin siyasar Senegal ke tunanin zai taimaka masa ya lashe zaben.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas