Zaben shugaban kasa a Tanzaniya
October 25, 2015Talla
Takara a zaben dai ta fi zafi ne tsakanin John Magufuli na jam'iyyar CCM da ke mulkin kasar da kuma tsohon firmaninstan kasar Edward Lowassa wanda wasu jam'iyyun adawa suke marawa baya.
Wata 'yar jarida a Tanzaniya din Sophie Tremblay ta shaidawa DW cewar mutane da yawan gaske sun fita rumfunan zaben da ta ziyarta kuma lamura sun wakana ba tare da wata matsala ba kana ba a samu wani rahoto na tashin hankali ba..
Nan da kwanaki hudu da ke tafe ne dai ake sa ran samun kamallen sakamakon zaben, sai dai gabannin haka ana yi jam'iyyar CCM hasashen samun nasara.