1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben Sudan ta Kudu a shekara ta 2015

Mohammad Nasiru AwalDecember 31, 2014

Kawancen kungiyoyin farar hula 75 a kasar Sudan ta Kudu ya bukaci mahukunta da su dage zabukan shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki

https://p.dw.com/p/1EDdn
Riek Machar und Salva Kiir
Hoto: Ashraf Shalzy/AFP/Getty Images

Kawancen kungiyoyin farar hula 75 a kasar Sudan ta Kudu ya bukaci mahukunta da su dage zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a shekarar 2015, suna masu nuni da rashin tsaro da rashin kyakkyawan yanayin siyasa. Sai dai a wani martani, mahukunta a birnin Juba sun ce za a gudanar da zabukan kamar yadda aka shirya a farkon watan Juli.

Kungiyar South Sudan Network for democracy and Elections wato SUNDE a takaice ta yi wannan kira na dage lokacin gudanar da zabukan. Ko da yake an shirya gudanar da zabukan a ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2015, fiye da watanni bakwai bayan lokacin da aka shirya da farko. Amma SUNDE da ke zama wani kawancen kungiyoyin farar hula 75 da ba ruwansu da siyasa a jihohi 10 na kasar Sudan ta Kudu, ta ce tabarbarewar tsaro da yanayin siyasa ba za sa samar da kyakkawan yanayin gudanar da zabe ba.

Südsudan - Abkommen
Hoto: Reuters

Sai dai kakakin fadar shugaban kasar Sudan ta Kudu Wek Ateng Wek ya yi watsi da kiraye kirayen dage lokacin zabukan, yana mai nuni da muhimmancin gudanar da zabukan a 2015.

Matukar aka gudanar zabukan kamar yadda aka tsara, to zai zama karon farko da kasar za ta zabi shugabanninta ta akwatin zabe, tun bayan da ta zama 'yantacciyar kasa a ranar 9 ga watan Julin shelarar 2011.

Symbolbild - Soldaten Südsudan
Hoto: Getty Images

Tun dai a ranar 15 ga watan Disamban 2013 Sudan ta Kudu ta tsunduma cikin yakin basasan, bayan da shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da wasu kusosin 'yan siyasa 11 da yunkurin kifar da gwamnatinsa. Kuma tarukan neman zaman lafiya a birnin Addis Ababa na kasar Habasha sun kasa kawo karshen fadan.