Girma ya fadi ga wasu manyan jam'iyyun siyasa a zaben Turai
May 27, 2019A sakamakon da aka bayyana na farko a daren jiya Lahadi zuwa yau Litinin na 'yan majalisun tarayyar Turai ya yi nuni da cewa jam'iyyun siyasa na masu ra'ayin 'yan mazan jiya masu goyon bayan hadin kan turan watau PPE na da kujeru 179 sabannin 216 da suke a majalsar baya. Sai masu ra'ayin gurguzu karfi na biyu na majalisar tarrayar Turan dake da kujeru 150 wanda a da suke da 185. Duk a cewar wadannnan gungun jamiyyun siyasar biyu na 'yan mazan jiya da masu ra'ayin gurguzu su ne ke da karfi a majalisar ta tarayyar Turai a halin da ake ciki ba su da karfin da za su samu rinjaye su biyu kawai domin amincewa da wasu kududrorin a majaliar sai sun yi kawance da wasu jamiyy.
Ana kyautata zaton cewar hadin gwiwar jam'iyyun siyasar masu ra'ayin 'yan mazan jiya masu goyon bayan manufofin Kungiyar EU za su yi kawance da jamiyyar masu fafutukar kare muhali wacce daga kujeru 52 a majalisar ta kai har kujeru 70 a yanzu sakamakon kyakyawar nasarar da ta samu a Tarayyar Jamus da Faransa da kuma 'yan Liberal a ciki har da na jami'yya Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron wacce ta samu kujeru 107 wanda a yayin da a can baya take da 69. A Faransar dai jam'iyyar masu kyamar baki Ta Marine Le Pen ta yi kusan kankan da jami'yyar 'yan mazan jiya ta RN Le Pen na da kishi 22.41 yayin da RN ke da kishi 23.31 a can Italiya kuwa jam'iyyar firaminista Matteo Salvini ta masu kishin kasa ita ce ke kan gaba yayin da suke da kujeru 58 sabannin 37 a baya.