1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma zaben 'yan majalisa a Isra'ila

Gazali Abdou Tasawa
September 17, 2019

Al'ummar Isra'ila na gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki domin zaben sabon Firaminista tsakanin 'yan takara biyu wato Firaminista Benjamin Netanyahu da kuma tsohon babban hafsan sojoji Benny Gantz.

https://p.dw.com/p/3Phjm
Israel | Parlamentswahlen 2019 | Wahllokal
Hoto: Reuters/C. Kern

Wannan zabe na zuwa ne watanni biyar bayan da a zaben 'yan majalisar dokokin da ya gudana cikin watan Afirilun wannan shekarar, kowanne daga cikin 'yan takarar biyu ya tashi da kujeru 35 a majalisar dokokin ta knesset mai kunshe da kujeru 120.

An dai bude runfunan zabe tun da misalin karfe bakwai na safe, inda masu zabe kusan miliyan shida da dubu 500 za su kada kuri'a a rumfunan zabe dubu 10 da 700 da aka tanada.

Bayan da Firaminista Netanyahu ya kasa kafa gwamantin hadin gwiwa ne dai biyo bayan zaben na watan Afrilu, ya dauki matakin rusa majalisar tare da kiran sabon zabe. Sai dai masu lura da harkokin siyasa a Isra'ilar, na ganin ko a wannan karo da wuya ta canza zani.