Zabiya na samun tagomashi a Kenya
December 20, 2017Muna cikin unguwar Kibera wata babbar unguwa ta masu karamin karfi a Nairobi inda sama da mutane miliyan daya suke zaune a daya daga cikin manyan titinan unguwar tsakanin wasu shagunan takalma a kwai wani shago mai lakanin ''Mzungu Reloaded'' inda ake sayar da katifu da jakunkuna, shagon ya samu wancan suna ne saboda sunan mai shagon Whycliffe Mzungu itadai kalmar Mzungu na nufin jar fata a harshen kswahili,kuma haka suke kiran turawa 'yan yawon bude ido, to amma Wycliffe ba bature bane illa wanda yake fama da lalura irin ta zabiya, a Afirika zabiya ba ya 'buya don haka suna fuskantar kyama da ga kuma zafin rana da yake cutar da fatar su ga raunin gani da ido,wannan ce tasa Wycliffe yake sanya hula hana sallah da kuma tabarau.
Wycliffe na daya daga cikin wadanda suka amfana da jari daga wata kungiyar Zabiya ta kasar Kenya mai rajin rage radadin talauci da samawa zabiya ayyukan yi da sana'oi da kuma wayar wa da jama'a kai, Daniel Moi wani zabiya kuma jami'ain wannan kungiya ya yi karin haske kamar haka.
Shirin wayar da kan al'umma kan zabiya ya fara samun nasara a 'yan shekarun nan don bayan yunkurin kungiyar Zabiya, gwamnatin kasar ta Kenya ta jajirce don canza wa alumma tunani akan Zabiya inda aka samar musu wani man shafawa a cikin sauki don rage musu raradin zafin rana a jikin su da ruguna masu dogon hannu da kuma tabarau.