1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba a zabukan 'yan majalisar Tarayyar Turai

Yusuf Bala Nayaya MNA
May 24, 2019

Sama da masu zabe miliyan 400 ne dai ake sa rai su kada kuri'a a Zaben EU na 'yan majalisar Tarayyar Turai su 751. Yayin da ake zura ido a ga rawar masu kyamar baki.

https://p.dw.com/p/3Izoa
Niederlande EU-Wahl
Hoto: picture-alliance/AA/A. Asiran

Yayin da aka shiga zabukan 'yan majalisar Tarayyar Turai, a wannan rana ta Juma'a al'ummar Ireland za su kada tasu kuri'ar bayan da aka shiga tantama kan makomar makotansu na Birtaniya saboda fafutukar kasar ta fita daga Kungiyar Tarayyar Turai yayin da a wasu kasashen na Turai ake tunanin 'yan fafutikar Turai sai 'ya'yanta za su girgiza siyasar ta nahiyar Turai.

Da misalin karfe bakwai, shida agogon GMT ne suka fara kada kuri'ar, haka nan al'ummar Jamhuriyar Chek suma za su fara kada tasu kuri'ar a zaben na kwanaki biyu, kwana guda bayan kada kuri'ar ta al'ummar Birtaniya. A can Holland kuwa jam'iyyar 'yan kwadago ta taka muhimmiyar rawa a nasarar da ke zama ba-zata inda ta mamayi kujeru da dama a zaben.

Firaministar Birtaniya dai Theresa May na kan katangar yiwuwar ajiye mukaminta saboda gazawarta wajen cika alkawura na fitar da Birtaniya daga EU har zuwa 29 ga watan Maris. Sama da masu zabe miliyan 400 ne dai ake sa rai su kada kuri'a a zaben 'yan majalisar Tarayyar Turai su 751.