Zakuna na fuskantar barazanar karewa a Afirka
October 27, 2015Sakamakon wani bincike da jaridar PNAS ta Amirka mai binciken kimiya ta gudanar ya nunar da cewa kusan kashi daya daga cikin biyu na zakuna dubu 20 da ke akwai yanzu haka a nahiyar Afirka na iya bacewa a cikin shekaru 20 masu zuwa.
Binciken wanda kungiyar ta PNAS ta share shekaru 20 tana gudanar da shi kan ayarin zakoki 47, ya nunar da cewa yawan zakunan na ragewa a kusan ko ina a kasashen nahiyar in banda a kasashen Kudancinta da suka hada da Baswana da Namibiya da Afirka ta Kudu da Zimbabuwe.
Kungiyar kasar ta Amirka da ke fafutkar kare namun daji ta nunar da cewa a tsakiyar karni na 20 da ya gabata adadin zakokin ya kai kimanin dubu 200 a nahiyar ta Afrika. Akasarin zakunan na mutuwa ne a sakamakon kisan da ake yi masu da ke da nasaba da barazanar da suke zamowa ga rayuwar al'umma da bisashen kiwo a wasu yankuna dama kuma amfani da ake yi da fatarsu wajen ado a wasu yankunan nahiyar.