1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaman dari-dari a Sudan ta Kudu

Gazali Abdou TasawaJuly 14, 2016

Shugaban kula da ayyukan tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu Herve Ladsous ya bayyana fargabar cewa a wannan karo, in rikicin ya barke zai yadu zuwa sauran yankunan kasar.

https://p.dw.com/p/1JOuu
Südsudan Opposition Soldaten
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Duk da cewa har kawo yanzu, bangarorin da ke gaba da juna na ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma, jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya ce wasu bayanan da suka samu na nuni da cewar dakarun bangarorin da ke gaba da juna a kasar na jan damarar yaki a yankin Arewacin kasar kusa da biranen Malakal da Leer. Kazalika ya ce a halin yanzu sojojin da ke biyayya ga gwamnati ke rike da iko a birnin Juba a yayin da mayakan 'yan tawaye su kuma suka ja daga a Yammacin birnin. A hannu guda kuma rahotanni daga Sudan ta Kudun na cewa wani ayarin motocin yakin kasar Yuganda dauke da manyan makamai ya kutsa cikin kasar da nufin ceto 'yan kasar ta Yuganda da yakin ya rutsa da su a birnin Juba.