Zanga zanga a ƙasar Senegal
January 27, 2012Talla
Hukumomin a ƙasar Senegal sun ci tuwon fashi sakamakon furcin da suka yi tun da farko na haramta zanga zangar yan adawa , kafin daga bisanni su ba da izini.To sai dai masu aiko da rahotannin na cewar hukomin sun yardda a gudanar da gamgami ne bayan da aka yi wata tattaunawa tsakanin jami'an gwamntin da na ƙungiyar Tarrayar Turai.
Nan gaba aka shirya majalisar tsarin mulki ta ƙasar zata baiyana cancantar takara shugaba Abdoulaye Wade a zaɓen shugaban ƙasar da za a yi na gaba a cikin wata mai kamawa.Yan adawa a ƙasar ta Senegal na cewar kuɗin tsarin mulki na ƙasar ya haramtawa shugaban mai shekaru 85 da haifuwa sake tsaya takara a wani wa'adi na ukku na mulki .
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu