1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga a birnin Kudus

Ahmed Salisu
December 8, 2017

Daruruwan Falasdinawa sun yi arangama da 'yan sandan Isra'ila a birnin Kudus lokacin da Falasdinawa suka fito don nuna rashin amincewarsu da ayyana birnin a matsayin babban birnin Isra'ila da Amirka ta yi.

https://p.dw.com/p/2p1v7
Jerusalem Proteste gegen die Verlegung der US Botschaft nach Jerusalem
Hoto: Getty Images/AFP/A. Gharabli

Wakilin kamfanin dillancin labaran AP da ya shaida faruwar lamarin ya ce Falasdinawa sun yi ta jifan jami'an tsaron da duwatsu yayin da su kuma suka maida martani da hayaki mai sa hawaye. Ya zuwa yanzu ba wani labari da aka samu na asarar rai. Can a kasashen Turkiyya da Malesiya da Iran da Somaliya ma dai an gudanar da zanga-zanga inda rahotanni ke cewar dubban mutane ne suka fantsama kan tituna don nuna fushinsu kana suka yi ta rera taken kin jinin Amirka da Isra'ila.