Zanga-zanga a Brazil ta janyo asarar rayuka
April 20, 2014Talla
Mazauna birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil da suka harzuka sun cinna wa motocin safa-safa wuta, domin nuna rashin jin dadi da kisan wasu matasa biyu da 'yan sanda suka yi, lokacin wata hatsaniya.
Masu zanga-zangar kimanin 30 sun toshe wata unguwa da ke birnin, abin da ya kawo cikas wa masu tafiya gudanar da bukukuwan Easter da mabiya addinin Kirista ke yi ko'ina a duniya. Mahukuntan kasar ta Brazil na ci gaba da daukan matakan karfafa harkokin tsaro yayin da rage kimanin watanni biyu a fara wasan neman cin kofin kwallon kafa na duniya da kasar za ta dauki nauyin shiryawa.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal