Zanga-zanga a Isra'ila ta neman zaman lafiya
March 4, 2015Talla
Masu gangamin sun yi shi ne da nufin tilasta wa duk wata gwamnatin da za ta zo kan mulkin bayan zaɓuɓɓukan da za a yi a ranar 17 ga wannan wata na Maris, da ta ba da fifiko ga shirin zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu.
Masu aiko da rahotanni sun ce duk da ruwan sama da aka riƙa sheƙawa kamar da bakin ƙwarya, wakilai na ƙungiyoyin mata sun kafe a bakin majalisar suna sauraran jawaban da aka gabatar.